IQNA

Ginin Hasumiya Mafi Tsawo A Duniya A Kasar Algeriya

21:11 - May 07, 2016
Lambar Labari: 3480391
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudanar da aikin babban masallaci mafi girma na kasar Algeriya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Guardian cewa, aikin gina babban masallacin kasar Algeriya na ci gaba da gudana, wanda ke da hasuminiya mafi tsawo a duniya, wadda tsawonta zai mita 265.

Wannan masallaci fadinsa zai mita dubu 20 murabba’i, kamar yadda kuma zai iya daukar masallata dubu 120 a cikinsa a lokaci guda, wanda hakan ya sanya ya zama masallaci mafi girm a atsakanin dukkanin masallatai na kasashen duniya.

Haka nan kuma masallacin zai kunshi babban dakin karatu, wanda shi ma zai dauki miliyoyin littafai na addini da kuma na bincike, kamar yadda zai hada da makaranta da wuraren koyar da alkur’ani mai tsarki.

Za a rika yin amfani da hanyar samar da karfin wutar lantarki ta hanyar hasken rana domin samar da wuta a wurin, da kuma samar da ruwa ta hanyar tara ruwan sama da tace shi domin yin amfani.

A cikin shekara ta 2017 ake sa ra kamala aikin wannan masallaci baki daya, haka nan kuma kudin da ake sa ran zai lakume baki daya za su kai dala biliyn 1.4 na Amurka.

3495494

captcha