Kamfanin dillanicn labaran iqna ya
habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yaum Sabi cewa, baya ga halartar
manyan limaman majami’oin Masar a lardin Aqsar Muhammad Badr gwamnan lardin
Aqsar da kuma Muhammad saleh wakilin ministan harkokin addini da sauran jami’ai
sun halarci wurin.
An gudanar da taron gasar ne a yankin Ridwan da ke tsakiyar birnin Aqsar.
Muhammad Saleh wakilin minister mai kula da harkokin addini a kasar ya bayyana cewa, gudanar da wannan taro na gasar hardar kur’ani mai tsarki yana da matukar muhimmanci tga al’ummar yankin da ma al’ummar Masar baki daya.
Ya kara da cewa halartar wasu daga cikin manyan limamai na wasu majamioi na lardin wata babbar alama ce da ke nuni da cewa al’umma suna zaune lafiya da junasu tare da fahimtar juna da kuma girmamawa.
Muhammad Badr gwamnan lardin ya bayyana cewa, gudanar da wannan gasa babban ci gaba ne gare su baki daya.
Abin tuni a nan dais hi ne, yankin Ridwaniyyah dai wuri da ake gudanar da tarukan addini tun lokacin marigayi Ahmad Ridwan, babban malami wanda aka yi a tsakanin shekara ta 1252 – 1329 Hijriyyah, kuma a 1965 tsohon shugaban masar Jamal Abdulnasir ya gina m,asallaci a wurin.
Dandalin Ridwaniyyah dai ya zama wani wuri na gudanar da addini domin raya koyarwar manzon Allah (SAW) da tarukan addini, kamar su Mab’as, tsakiyar sha’aban, daren Qadr da sauransu.