Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin
sadarwa na yanar gizo na standart digital cewa, Umar Hassan ya bayyana ahakn ne
a lokacin da yake halartar wani taro na addini a yankin na Mombasa, wanda ya
samu halartar baki daga kasashen Burkina Faso, Nigeria da kuma India.
Inda yana yin kira matasa yan asalin kasar ta Kenya da suka shiga wanann kungiya da su yi ma kansu kiyamullali su dawo gida domin su samu afuwa daga gwamnati.
Ya ce idan msuulmi bai san addininsa ba to ko shakka babu abin da yake yi wani abu ne daban ba msuulmi ba, kuma rashin sanion addini ne ke kai matasa ga shiga wadanann kungiyoyi.
Daga karshe ya bayyana cewa addinin muslunci addinin zaman lafiya da fahimtar juna da yin ragwame ne, saboda haka ya kamata musulmi su yi riko da irin wannan sahihiyar koyarwa ta muslunci.