Kamfanin
dillanicn labaran Iqna ya nakalto daga bangaren sadarwa na hubbaren cewa, an
samar da wani wuri na musamman na kula da ayyukan tsaro na wannan hubbare wanda
zai rika kula da kamarori 800 na zamani.
Sheikh Abdulmahdi Alkarbala’i shi ne mai kula da ayyukan hubbare na Imam Hussain (AS) ta fuskar shari’a, ya bayyana cewa hakika wannan aiki yana da matukar muhimmanci, kuma hakan zai bayar da damar gudanar da ayyukan tsaro da kuma kare rayukan jam’a masu ziyara a wannan wuri.
Daga karshe ya bayyana cewa, wannan aiki ya gudana sakamakon hadin gwaiwar da aka samu a tsakanin hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren Abul fadl Abbas (AS) da suke ksa da juna.