Bangaren
siyasa, a cikin wani umurni da ya
bayar, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada
Dakta Abdul'ali Ali Asgari a matsayin sabon shugaban hukumar gidan radiyo da
talabijin ta Iran bayan ya amince da murabus din da tsohon shugaban hukumar
Muhammad Sarafraz yayi ne.
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin jagora fassasar matanin wannan sako na jagora kamar haka:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Mai girma Dakta Abdul'ali Ali Asghari (Allah Ya kara masa nasara).
Bisa la'akari da murabus din da Malam Muhammad Sarafraz yayi da kuma mika godiya a gare shi saboda irin gagarumin kokari na juyin juya hali da kishin da ya nuna wanda bai kamata a mance da hakan ba, sannan kuma saboda irin tsohon tarihin da kake da shi na riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci da kuma kwarewa ta shugabanci a hukumar watsa labarai ta kasa, don haka na nada ka a matsayin shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin.
Abin da ya kamata in sanar da kai, yana nan cikin takardar da na ba wa Malam Sarafraz a lokacin da na nada shi (wannan matsayin). A saboda haka ina kara jaddada maka muhimmancin yin tsare-tsare, kiyaye manyan siyasosi na kasa, janyowa, kiyayewa da kuma tarbiyyantar da ma'aikata ma'abota juyin juya hali da kuma aiki tukuru bugu da kari kan yin tasiri a fagagen watsa labarai na zamani, sannan da kuma dogaro da Allah Madaukakin Sarki.
Ina roka maka maka taimako Allah Madaukakin Sarki da dacewa cikin wannan aikin.
Sayyid Ali Khamenei
22, ga watan Urdebehesht, 1395
(11 ga watan Mayu, 2016)
NB
Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya nada Malam Sarafraz a matsayin memba na dindindin a majalisar koli mai sanya ido kan kafafen watsa labarai na zamani. Kafin nada shi a matsayin shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin din, Malam Sarafraz ya kasance memba wanda ba na dindindin ba a majalisar.