Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo elbilad.net cewa, wannan taro na Alhoilaliya yana samn halaertar masana
daga kasar ta Algeriya, da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi da na
larabawa.
Babbar manufar taron dai it ace yin dubi kan matsin dakunan karatun kur’ani da ake da su a kasashen musulmi na tarihi da suke bayar da gudunmawa ta fuskoki da dama.
Munir Talili daga jami’ar Zaituna ta kasar Tunisia, Muhammad Wuld Alda daga jami’ar Mauritania, Lui Isa jakadan Palastinu a kasar Algeriya, suna daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wurin.
Masu bayanai sun ce a wurin, ya zama wajibi musulmi su mayar da hankali wajen karfafa lamurran kur’ani da kuma yadda za a kyautata su, musamman ta fuskar karatu da kuma warren karatun.
Kasar Algeriya dai na daga cikin kasashen da suka gina dakunan karatun kur’ani na gargajiya tun daruruwan shekarun da ska gabata, har zwa lokutan yaki tsakanin kasar da Faransa, a cikin shekara a 1954 zuwa 1962.