IQNA

Zul-Fiqar Na Hizbullah Ya Yi Shahada

22:38 - May 13, 2016
Lambar Labari: 3480407
Bangaren kasa da kasa, Mostafa Badruddin daya daga cikin manyan kwamandojin Hizbullah yay i shahada a kusa da birnin Dasmacus na Syria.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Press TV cewa, Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa babban kwamandan bangaren sojinta Shahid Mustafa Badruddeen yayi shahada sakamakon wani harin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai wa daya daga cikin cibiyoyinta da ke kusa da filin jirgin saman birnin Damaskus na kasar Siriya.

Kungiyar ta Hizbullah ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar yau Juma'a inda ta ce cikin dukkanin alhari take sanar da shahadar babban mujahidi Shahid Mustafa Badrudden (wanda aka fi sani da Sayyid Zulfiqar) sakamakon wani hari da aka kai wa cibiyar kungiyar da ke kusa da filin jirgin saman Damaskus, na kasar Siriya.

Sanarwar ta kara da cewa shi dai Shahid Badrudden yana kasar Siriyan don jagorantar fadar da kungiyar take yi da kungiyoyin 'yan ta'adda masu kafirta musulmi da aka shigo da su kasar Siriyan don cimma manufofin Amurka da yahudawan sahyoniya a yankin Gabas ta tsakiya.

Har ila yau sanarwar ta ce tuni ta fara gudanar da bincike don tantance yanayin harin, tana mai cewa a nan gaba za ta yi karin haske kan lamarin.

Shi dai Shahid Badrudden ya zama kwamandan sojin kungiyar ta Hizbullah ne bayan shahadar tsohon kwamandan sojin Shahid Emad Mughniyya wanda haramtacciyar kasar Isra'ilan ta kashe a kasar Siriya a shekara ta dubu biyu da takwas.

3497474

captcha