IQNA

Wakilin Oman A Gasar Kur’ani:

Riko Da Koyarwar Kur’ani Ita Ce Babbar hanyar Yaki Da Akidar Takfiriyyah

22:43 - May 13, 2016
Lambar Labari: 3480409
Bangaren kasa da kasa, mai wakiltar kasar Oman a gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya a Iran ya bayyana cewa riko da koyarwar kur’ani ne hanyar yaki da akidar ta’addanci ta Takfiriyyah.
Ahmad Bin Naser Al-qannubi mai wakiltar kasar Oman a gasar karatu da hardar kur’ani ta duniya karo 33 a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya bayyana cewa riko da koyarwar kur’ani da sunnar manzon Allah (SAW) ne hanyar yaki da akidar ta’addanci ta Takfiriyyah da murkushe ta.

Ya ce babban abin takaici ne yadda wasu yan tsiraru da suke bata sunan musulmi suka zama su ne abin auna musulunci da su a duniya, wanda hakan ya zama hujjar bata sunan wannan addini na zaman lafiya.

Al-qannubi ya ce wannan shi ne karon farko da ya taba halartar wata gasa amatsayi na kasa da kasa, kuma shi ne karon farko da ya zo Iran, amma hakan y aba shi damar kara samun gogewa ta fuskoki da dama.

Ya kara da cewa akasarsa yana halartar gasar kasa baki daya ta sarki Qabus, wadda duk shekara ake gabatar da ita, kuma yana da cikin wadanda sukan samu nasara a gasar a lokacin gabatar da ita.

3497430

captcha