Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga
shafin Alalam cewa, sheikh Na’im Kasim ya bayyana cewa, kungiyar Hizbullah za
ta ci gaba da riko da tafarkin gwagwarmaya yana mai cewa nan da wani lokaci
kadan kungiyar za ta sanar da sakamakon binciken da ta gudanar dangane da harin
da aka kai wa babban kwamandan sojinta Shahid Mustafa Badruddeen a kasar Siriya
da yayi sanadiyyar shahadarsa.
Sheikh Qasim ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a wajen jana'izar shahid Badruddeen a yammacin yau a birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon inda ya ce wannan hari da aka kai da yayi sanadiyyar shahadar babban kwamandan sojin kungiyar Hizbullah din shahid Mustafa Badruddeen (Sayyid Zulfiqar) ya faru ne kusa da filin jirgin saman birnin Damaskus (babban birnin kasar Siriya) kusa da daya daga cikin cibiyoyin kungiyar ta Hizbullah, yana mai cewar 'yan kungiyar suna ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin harin da kuma dalilinsa.
Sheikh Na'im Qasim ya ci gaba a halin yanzu dai kungiyar ba za ta yi riga malam masallaci wajen dora alhakin hari kan kowa ba har sai ta jira an gama binciken, wanda ya ce cikin 'yan sa'oi masu zuwa kungiyar za ta sanar da sakamakon binciken.
Yayin da yake magana kan shahid Mustafa Badruddeen kuwa, Sheikh Na'im Qasim ya bayyana shi a matsayin babban kwamandan dakarun kungiyar ta Hizbullah wanda haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda masu kafirta musulmi suka fuskanci gagarumin bugu da kuma dandana kudarsu a hannunsa.
Sheikh Qasim ya kara da cewa Shahid Badruddeen ya sadaukar da rayuwarsa ne a kan tafarkin jihadi yana mai cewa ba zai taba dawowa daga Siriya ba face ko dai a matsayin shahidi ko kuma yana dauke da tutar nasara.
Shi dai Shahid Badrudden, dan shekaru 55 a duniya ya zama kwamandan sojin kungiyar ta Hizbullah ne bayan shahadar tsohon kwamandan sojin Shahid Emad Mughniyya wanda haramtacciyar kasar Isra'ilan ta kashe a kasar Siriya a shekara ta 2008. Sannan kuma ya tafi kasar Siriya ne don jagorantar dakarun kungiyar Hizbullah din da suke taimakon gwamnatin Siriya wajen fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da aka shigo da su kasar Siriyan.