IQNA

Wasu Bata Gari Sun kai Hari A Massalci A Nigeria

21:11 - May 14, 2016
Lambar Labari: 3480411
Bangaren kasa da kasa, wasu zaune banza sun kaddamar da hari kan wani masallaci a garin Lagos na Najeriya.
Kamfanion dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «Avvo.com» cewa, wasu mutane zaune gari banza dauke da makamai sun kaddamar da harin a kan masallacin ne a lokacin da ake gudanar da salla a cikinsa a birnin na Lagos.

Majiyoyin ‘yan sanda a birnin sun bayyana cewa, mutanen da suka kaddamar da wannan harin sun kafa wata kungiya ta yan daba da ta sabawa kaida da doka, wanda hakan yasa a ka kame su, amma an sake bayan da aka karbi belin nasu.

Bayan fitowarsu sun fara da kai hari kan masallaci a lokacin mutane suke salla, duk kuwa da cewa babu wanda ya rasa ransa ko jikkata, amma sun bata bangayen masallacin.

3497948

captcha