IQNA

Tarjamar Nahjul Balagha a Cikin harshen Senegal

21:12 - May 14, 2016
Lambar Labari: 3480412
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da tarjamar littafin Nahjul Balagha a cikin Wolof bias himmar karamin ofishin jakadancin Iran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na dakar.icro cewa, Sheikhuna Lauh shugaban darikar muridiyyah a kasar Senegal ya gana da karamin jakadan Iran a kasar Sayyid Hassan Heshmatim, inda ya tabbatar masa da fara gudanar da wannan aiki.

Sheikhuna Lauh y ace hakika ya ji dadin yadda ya kasance mai tarjama kalmomin Imam Ali (AS) daga littafin Nahjul Balagha, kasantuwar hakan babban abin alfahari gare shi, kuma hakan yana zaman Karin haske ne gare shi.

Sheikhuna Lauh ya kasance daya daga cikin bakin da aka gayyata zuwa gasar karatun kur’ani ta duniya a birnin Tehran a matsayin daya daga cikin baki na musamman.

Ya tarjama kur’ani mai tsarkia cikin harshen Wolof wanda kasar Libya ta dauki nauyin buga su tare da raba a masallatai da ke kasashen Afirka.

3497859

captcha