
Kamfanin dillancin labaran iqna ya baharta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanargizo na Petra cewa, zaman taro dai zai mayar da hankali kan yaki da akidsar takfiriyyah ta ta’addanci da ke bata sunan muslunci a duniya ne.
Wannan zaman tarodai babbar manufarsa it ace samar da hanyoyi da ya kamata musulmi su amfani da su domin tunkarar wannan mummunar akida ta takfiriyyah, wadda it ace tushen duk wani aiki na ta’addanci da sunan addini.
Daga cikin kasashen da wakilnasu za su halrci taron akwai Masar, Palastinu, Yemen, Thailand, Nigeriya, Lebanon, Austria, Faransa, Ukraine, Sweden, Pakistan, Kuwait, Malaysia, Morocco, da iraki.
Za a gudanar da zama 4 ne a taron, inda za a duba makaloli guda 16 wadanda suka yi Magana tare da bayar da mahanga kan yadda ya kamata a tunkari wannan mummmunar akida ta ta’addanci a duniya baki daya.