IQNA

Mai Tarjamar Wakokin Imam Khomeni (RA) A Harshen Georgia Ya Rasu

23:42 - May 16, 2016
Lambar Labari: 3480416
Bangaren kasa da kasa, Professor Magali Todva masani kan harkokin Iran kuma wanda ya tarjama wakokin Imam Khomenei (RA) ya rasu.
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa Professor Magali Todva ya rasu yana da shekaru 89 a duniya, ya kuma gudanar da ayyuka na ilimi ta fuskoki da dama.

Shafin yanar gizo na bangaren ofishin yada ala’adu na kasar Iran Georgia ne ya bayar da wannan bayani.

A kasar Georgia daya daga cikin masu tarjamar wakokin marigayin Imam Khomeni (RA) almajirin Professor Magali Todva ne, wanda shi ma ya bayar da gudunmawa ta fuskar tarjama kalaman adabi na marigayin da kuma wakokinsa zuwa harshen kasarsu.

Professor Magali Todva ya rubuta littafai da dama kamar yadda kuma ya tarjama wasu da dama, musamman na fitattun masana da mawakan kasar Iran, daga cikin kuwa har da littafin wakokin maulana.

Kamar yadda kuma ya tarjama wani littafi da ke Magana kan sarakunan da aka yi a kasar na tsawon zaunna wadanda suka kafa masauratu masu cin gishin kans a tarihi.

A cikin shekaru arba’in da suka gabata Professor Magali Todva ya rubuta littafai a bangarori daban-daban, kamar yadda ya tarjama wasu a cikin harsunan farisanci da kuma rashanci.

3498576

captcha