IQNA

Bikin Tunawa Da Quds A Kasar Tunisia

23:45 - May 16, 2016
Lambar Labari: 3480417
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da bikin tunawa da Quds ta hanyar ayyukan fasaha a birnin Tunis na kasar Tunisia.
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tunis.icro cewa, wannan biki ana gudanar da shi tare da hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin palastinawa masu ayyukan fasa da kuma cibiyar bin Arus ta kasar Tunisia.

Mawaka da masu ayyukan fasaha na kasar Tunusia suna halartawa wurin gudanar da wannan taro, kamar yadda su ma palastinawa da sauran larabawa mazana kasar ba a bar su a bay aba.

Malama samira Khal;fi wadda ita babbar darakta da ta shirya taron, a lokacin da take ganawa da Malam Asadi Muwahhad wakiliyar Iran awurin, ta bayyana jin dadinta matuka dangane da yadda aka bayar da muhimmanci ga wannan batu na Palastinu.

3497810

captcha