Kamfanin dillancin labaran Iqn aya
habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da gasar kur’ani ta dniya karo na
talatin da uku, ana kuma gudanar da gasar masu nakasa ta kasa da kasa.
Ita dai wannan gasa ana gudanar da ita ne a babban masallacin marigayi Imam kamar dai yadda ake gudanar da gudar gasar a nan.
Abdulgafur Jauharchi daga kasar Iran shi ne ya zo na daya, sai kuma Ahmat Sarikaya daga Turkiya da kuma Sabirin Muhammad Zu’aibi daga kasar Tunisia, su ne suka na biyu da kuma na uku.
Wannan gasa tana gudana ne a babban masallacin marigayi Imam Khomenei (RA) da ke birnin Tehran, tare da halartar dukkanin wakilan da suka wakilci kasashensu.
A gobe ne dai ake kamala wannan gasa, inda za a bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo, da ma saran dukkanin wadanda suka halrci gasar.