
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, alkalan da suke gudanar da alkalanci a gasar kur’ani ta duniya karo na 33 a jamhuriyar musulunci ta Iran sun sanar da sakamakon karshe na gasar a bangarorin hardar dukkanin kur’ani da kuma karatu kamar haka:
Bangaren hardar dukkanin kur’ani
Mujtaba Fadfani daga Iran
Abdulaziz Ahmad daga Masar
Muhammad Ali Abdullah daga Australia
Khalid Sankari daga Ivory Coast
Muhammad tahir Hassan daga Niger
Sai kuma bangaren karatun kur’ani
Hamid Walizadeh daga Iran
Muhammad Javid Akbari daga Afghanistan
Bahruddin Said daga Indonesia
Sayyid Abbas Ali daga Jamus
Mustafa Ali daga Holland
Sakamakon wannan gasa dai ya zo daidai da abin kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna yay i hasashe.
Abin tuni a nan dais hi ne, wannan gasa ta duniya karo na 33 ta gudana ne a babban masallacin marigayi Imam Khimenei (RA) tare da halartar wakilan kasashe fiye da 70 na duniya.