
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kwalejin ayyukan kiwon lafiya a jami’ar harward cewa, sakamakon bincike da aka gudanar ya nuna cewa mata masu halartar tarukan addini ba sui cika saurin kamuwa da cutuka masu saurin kisa ba, kamar ciwon daji ko zuci ko abin da yay i kama da haka.
Tailor Windrowill malama ce a wannan bangre na bincike kan lamurran lafiya awannan jami’a, wadda kuma it ace ta jagoranci gudanar da wannan bincike, wanda ya tabbatar da cewa halartar tarukan addini ga m,ata yana yi musu tasiri wajen kara tswon rayuwarsu.
Ta ce wasu daga cikin mahalrta taron sun yi imanin cewa, masu ta’amulli da wasu abubuwa kamar taba da saransu, suna yin hakan ne domin samun sauki dda jin dadi a cikin rayuwa, da kuma samun saukin matsaloli.
Sakamakon binciken dai ya nuna cewa kiman kasha 40 cikin dari na Amurkawa suna halartar tarukan addini sau dau ko fiye da ahaka acikin mako.