
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa wannan zama za a gudanar da shi ne karkashin jagorancin Sheikh Nazzar Aljiyali Sheikh Almukashifi minister mai kula da harkokin al’adun muslunci a kasar.
Taron zai samu halartar wakilai na tawagogi daga kasashen Saudiyya, Masar, Kuwait, Qatar da kuma Turkiya, gami da wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka.
A kowane zama na shekara dai akan tattauna muhimamn batutuwa da suka danganci kasafin ayyukan wanann cibiya ne da za a gudana ra cikin shekara.
Dukkanin masu halartar zaman dai sukan yi alkawalin wasu kudade na gudar da ayyukan da za ayio na shekara.
An kafa wannan babbar cibiy ta buga kur’ani da ake kira mushafin Afirka tun a cikin shekara ta 1994, kuma ya zuwa yanzu ta buga kur’anai da kwafinsu ya kai miliyoyi, wadanda ake raba su ga musulmi.
Kwamitin amintattun dai ya kunshi mambobi guda 45 ne, da suka fito daga kasashe daban-daban, wadanda suke suke da alhakin duba dukkanin ayyukan cibiya da kuma sanar da abin da ya kamata aaiwatar.