
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Maan cewa, Atinger an tsare shi a gidan kaso na tsawon watanni 8 ba tare da an yanke masa hukunci ba, kuma kotu ta bayar da umarnin sakinsa
A cikin barazar da ta gabata ce wannan bayahude mai shekar 24 da ya haihwa ya agoranci kai farmaki kan wani gidan palastinawa, inda ya kasha ba da uwa da kuma wani karamin yaro dan watanni takwas da haihuwa.
Haka nan kuma wasu rahotanni sun shi ne wanda ya jagoranci wani farmakin yahdawa masu tsatsauran ra’ayi kan wata majamiar mabiya addinin kirista a bara.
Wanann bayahude dai yana samun goyon baya da kariya daga jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila a kan dukkanin ayyukan ta’adanncin da yake aikatawa.