IQNA

Hankoron Samun Hutu A Makarantu A Ranakun Idin Musulmi A New Jersy

23:53 - May 19, 2016
Lambar Labari: 3480429
Bangaren kasa da kasa, iyayen yara muslmi da suke karatu a makarantu a jahar New Jersy ta kasar Amurka sna hankoron ganin sun samu hutu a ranakun idin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NJ cewa, wasu daga cikin iyayen yara muslmi da suke karatu a makarantu a jahar New Jersy ta kasar Amurka sna hankoron ganin sun samu hutu a ranakun idin musulunci na shekara.

Babban abin da iyayen ke fatan gani shi ne,a mayar da ranakun hutun a hukmance, ta yadda dalibai za su samu damar yin tarukan idi kamar yadda sauran mabiya addinai suke a ranakun hutu da ake bas u.

Wasu daga cikin jahohin kasar Amurka sun amince da su bar ranakun idin muslunci a matsayin ranakun hutu a gare su a hukumance, domin bayar da dama ga musulmi dalibai su yi idi.

Yanzu haka dai a mahukunta abagaren ma’aikatar ilimi ta wannan jaha ta karbi wasukun da iyaen musulmi suka rubuta, kuma an ba su lokaci da za a gudanar da bahasi kan lamarin daga bisani a basu amsa.

Kasar Amurka dai tana daya daga cikin kasashen da musulmisuke fuskantar matsaloli a halin yanzu sakamakon hare-haren ta’addanci da masu dauke da akidar karfirta musulmi suke kaiwa da sunan addinin muslnci, wanda kuma hakan yake shafar wadanda ba su ji ba su gani ba.

3499377

captcha