IQNA

‘Yan Ta’adda Sun Bata Sunan Addinin Muslunci

22:37 - May 21, 2016
Lambar Labari: 3480434
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar ya bayyana cewa yan ta’adda masu da akidar kafirta muslmi sun bata sunan muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadsarwa na yanar gioz na Vision cewa, Ahmad Tayyib yayin ganawa da wasu daraktoci 40 na kafofin yada labarai daga kasashe 23 na Afirka a jami’ar Azahar a Alkahira, ya bayyana cewa yan ta’adda masu da akidar kafirta muslmi sun bata sunan musluncia duniya.

Ya ce addinin muslunci addinin zaman lafiya ne da yafiya, ta yaya za a yi wanann addini ya yi umarni da ta’addanci?

Tayyib ya kara da cewa, babbar hanyar yaki da ta’addanci a halin yanzu ita koyar da addinin muslnci bisa hakikaninsa, da kuma wayar da kan matasa kan gurbatacciyar fahimtar da ake cusa musu dangane da addinin da suna jihadi.

Ya yi gargadin cewa, idan har ba ayi hakan ba, to kuwaan amanar wannan addini, kuma mahaliccinmu ba zai kyale mu ba kan hakan.

Abin tini a nann dais hi ne, cibiyar Azahar tana da dalibai fiye da dubu dari tara da suke karatu a cikinta, kuma it ace cibiyar addini mafi gira da jima a a cikin kasashen musulmi.

3499996

captcha