IQNA

Gasar Kur’ani Ta Iyalai A Karon Farko A Kuwait

23:39 - May 22, 2016
Lambar Labari: 3480436
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri na gasar kur’ani mai tsarki a karon farko a kasar Kuwait wadda ta shafi iyalai kawai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 3robanews.com cewa, cibiyar kula da ayyukan shari’ada ska shafi iyalai ce za ta dauki nayin gudanar da wannan gasa akaron farko a cikin kasashen Khalij.

A cikin wannan gasa za a fitar da mataki na dukkanin iyalai da za su halarta baki daya.

Cibiyar tya bayar da bayanin cewa, a halin yanzu ana cikin gudanar da dukkanin shirin da ya kamata, amma gasar za a gudanar da ita ne a cikin watan Ramadan.

Yusuf Salim Al-sumai shi ne babban darakta da ya shirya wannan shiri tare da daukar nauyinsa, ya bayyana cewa gasar za ta hada da mata da kuma maza, wadanda suka yi rijista tare da iyalansu, kuma za a bayar da cikakken bayani kan gasar kafin azumi.

Kamar yadda kuma shirin zai shafi shirya zaman masallaci da ya kebanci mata kawai, kuma zai ci gaba har zuwa ranar 19 ga watan na Ramadan mai alfarma.

3499889

captcha