IQNA

Sa’oi Nawa Ne Misrawa Za Su Yi Azumi A Wannan Shekara?

23:41 - May 22, 2016
Lambar Labari: 3480437
Bangaren kasa da kasa, wasu masu ilimin taurari sun bayyana cewa a wannan shekara Misrawa za su yi azumi na sa’oi 464 da kuma mintuna 77.

Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nujum Misriyyah cewa Hatam Audah wani masani kan harkokin taurari da hisabi ya bayyana cewa a wannan shekara watan Sha’aban zai kare a rana ta 29 ne.

Ya ce Ranadan na wannan shekara zai fara ne daga ranar 6 ga watan yuni, kuma kasar Masar na daga cikin kasashen da za su fara azumi a ranar wanda zai kai tsawon sa’oi 15 da mintuna 49 a kowace rana.

Haka nan kuma ya kara da cewa azumin bana Masar a ranar da tafi tsawo it ace sa’oi 15 da mintuna 52 sai kuma mafi gajarta ita ce sa’oi 15 da mintuna 45 a rana.

Auda ya ce a wannan shekara Misrawa za su yi azumi na sa’oi 464 da kuma mintuna 77.

3500165

captcha