
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Country of zero cewa, gungun masu adawa da muslunci sun gudamnar da wata zanga-zangar kyamar muslunci a garin.
Bayanin ya ce mutanen sun bayyana cewa sn yi hakan ne domin su nuna irin canjin da aka samua cikin tunainsu dangane da muslunci, inda ska ce sun gane addinin muslunci cewa addinin ta’addanci ne da tashin hankali.
A daya bangaren kuma an shirya cewa masu adawa da wannan zanga-zangar ta masu kyamar muslunci su za su gudanar da nasu gangamin da zanga-zanga domin goyon bayan yan tsiraru marassa rinjaye a kasar, da suka hada har da musulmi.
Jami’an tsaro a cikin kayan sarki dai sun zama cikin shiri, domin ganin ganin cewa ba a samu tashin hankali ko taho mu gama a tsakanin bangarorin biyu ba.