
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na Anatoli cewa, jami’an tsaron kasar Turkiya sun mayakan kurdawa na PKK sun harba makamai a kan wani masallaci a garin Sharnaq na kasar Turkiya, wanda hakan yay i sanadiyya konewar kur’anai.
Yayin su kuma a nasu bangare mayakan kurdawa suka ce sun tayar da bam din ne a kusa da masallacin domin hana sojojin Trkiya da mayar da su baya, amma hakan ya shafi masallaci ba tare da nufin yin hakan ba, inda har wasu daga cikin kur’anai a masallacin suka lalace.
Bayanin ya ci gaba da cewa sojojin Turkiya sun shiga cikin masallacin, kuma sun mayar da kwafin kur’anai da ke wurina cikin kantoci.
Tun daga ranar 14 ga watan Maris na wannan shekara ne sojojin Turkiya suka fara kaddamar da farmaki kan makan kurdawa na PKK, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama daga bangarorin biyu.