IQNA

22:03 - May 23, 2016
Lambar Labari: 3480442

Desh Ta Dauki Alhakin Harin Syria

Bangaren kasa da kasa, kngiyar Daesh ta dauki alhakin harin ta’addanci a kan biranan Tartus da Jabla na kasar Syria.

Desh Ta Dauki Alhakin Harin Syria

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin press TV cewa an tayar da wasu jerin bama bamai a cikin mota sannan kuma an kai hare-haren kunar bakin-wake a birane biyu da ke gabar teku a yankin Latakia da ke hannun gwamnatin Syria.

Masu fafutuka sun bayyana cewa mutum fiye da 100 sun mutu bayan fashewar wasu abubuwa kusa da tasoshin motocin safa a Tartous da kuma Jableh wadanda a baya ba sa cikin jerin wuraren da ake rikici.

An kuma bayar da rahoton cewa an kai wani hari a wani asibiti a Jableh.

Wata kafar yada labarai ta kungiyar mayakan IS ta yi ikirarin kai hare-haren.

Rasha, wacce take marawa Shugaban kasar baya, na da sansanin sojin ruwa a Tartous, yayin da sansaninta na sama ke kusa da Jableh.

Wani kakakin gwamnatin Rasha, ya ce hare-haren na nuni da bukatar ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a Syria.

Rasha ta fara kaddamar da hari kan sansanonin yan ta’adda a cikin kasar Syria tare da izinin gwamnatin kasar, wanda hakan ya karya lagon yan ta’adda matuka, kuma shi ne babban dalilin da ya sanya suke daukar matakan kai harin bam a halin yanzu a cikin wadannan yankuna.

3500413

captcha