Kamfanin
dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar
gizo na Business Standard cewa, wasu mutane ne dauke da makamai suka kaddamar
da harin a lokacion da mutane suke gudanar da sallaa cikin masallaci a garin Aljaninah.
Mutanen an adanganta su da masu dauke da makamai da ke kaddamar da farmaki a cikin yankin Darfur da ke yammacin kasar ta Sudan, wanda kuma wannan bas hi ne karon farko ba.
Babban abin da ke ci ma mutanen wannan yanki na Aljaninah tuwo a kwarya dais hi ne fada na kabilanci, wanda ya zuwa yanz ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da tserewar wasu daga yankunansu.
Kasar Sudan dai na daga cikin kasashen nahiyar wadanda ke fama tashin hankali na kabilanci, wanda kuma hakan ne ma yay i sanadiyar raba kasar tsakanin arewa da kdanci, ana zargin gwamnatin Sudan da gallazawa sauran mutane wadanda ba larabawa ba.