IQNA

Sharik Zafar:

Hana Musulmi Shiga Amurka ya Saba Dokokin kasar

23:57 - May 24, 2016
Lambar Labari: 3480445
Bangaren kasa da kasa, wakilin musulmia ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana ikirarin da Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka ke yi kan hana musulomi shiga kasar da cewa ya saba dukkanin dokokin Amurka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «THE STRAITSTIMES» cewa, Sharik Zafar wanda shi ne wakilin musulmi a ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana furucin da Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka ke yi kan hana musulomi shiga kasar idan ya ci zabe da cewa, wanna kalami ya saba dukkanin dokokin kasar baki daya.

Sharik Zafar y ace a cikin dokokin Amurka babu inda aka ce a hana wani mutum shiga a cikin kasarsa saboda addininsa ko mahagarsa ta addini.

A kan haka ya ce; irin maganganu da Donald Trump ken a nuna tsananin adsawa a kan mabiya addinin muslunci suna da matukar hadari, domin hakan yana haifar da kiyayya kan musulmi a kasar saboda addininsu.

Ya kara da cewa bababr hanyar hana wannan mummunar dabi’a ta kyamar muslmi it ace tattaunawa tare da fahimtar da masu wannan akida hakinin msulunci.

3500342

captcha