
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, Taha Muhamamd Abdulwahab ya karyata batun mutuwar Mahmud Sadiq Munshawi da ake yadawa a wasu kafafen yada labarai.
Ya ce sun yi Magana da was daga cikin almajiransa wadanda suke karatu karkashinsa sun tabbatar masa da cewa wannan labara bas hi da wani tushe.
Taha Abdulwahab y ace ko shakka babu Mahmud Munshawi ya dauki dogon lokaci yana fama da rashin lafiya, kuma har yanzu yana can a kwance yana jinya.
Ahmad Ahmad Nu’ainua shi ma makaranci ne fitacce a kasar ta Masar kuma aboki ga Munshawi, ya karyata wannan labara.
Kafin wannan lokacin dai an ta yada labaraia kafofin sadarwa na yanar gizo da ke cewa Mahmud Munshawi Allah ya yi masa rasuwa.
Malam Mahmud Munshawi babban abokine ga marigayi Muhammad Sadiq Munshawi, kuma dukkaninsu yan garin Munsha na kasar, wadanda suka yi karatu tare kuma suka yada koyarwar kur’ani mai tsarki mai tsarki.