IQNA

An kama Wani Mutum Na Shirin Tayar Bam A Kazimain

22:54 - May 26, 2016
Lambar Labari: 3480450
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Iraki sun cafke wani mutum a lokacin da yake shirin tayar da bam a cikin hubbaren Kazimai.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Saumaria cewa, an kame mutumin ne a lokacin da ya shiga cikin garin kafin kaiwa ga hubbaren mai tsarki.

Masu amfani da kafofin sadarwa na yanar gizo sun saka hoton mutumin da bama-bamaia jikinsa da yake da shirin tayar da su a cikin hbbaren mai tsarki da ya samu damar yin hakan.

Shakir Jaudat babban jami’in yan sanda a yankin Bagdad ya bayar da bayani dangane da yadda wani dan sanda ya kame wannan dan ta’adda.

Haidar Abadi Firayi ministan kasar Iraki ya bayar da umarnin kara girma ga dan sandan da ya kame wani babban dan ta’adda kafin ya kai ga tayar da bam da ke jikinsa a kan fararen hula.

Kazimain dai wani wuri ne da ke cunkoson jama’a a kusa da birnin Bagadaza, wanda kuma a nan hubbarori biy na Imam Kazim (AS) da Imam Jawad (AS) suke.

3501175

captcha