IQNA

Jagora Juyin Islama:

Manufar Kutsen Makiya Ita Ce Raunana Juyi Daga Cikin Gida

23:43 - May 27, 2016
Lambar Labari: 3480452
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da kuma membobin majalisar kwararru ta jagoranci ta kasar Iran karo na biyar ya bayyana cewar ci gaba da wanzuwa da kuma ci gaban tsarin Musulunci da kuma tabbatar da manufofin juyin juya halin Musuluncin shi ne "samun karfi na hakika a jamhuriyar muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora tarjamar wannan matani cewa, a safiyar yau Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da kuma membobin majalisar kwararru ta jagoranci ta kasar Iran karo na biyar, inda yayin da yake karin haske dangane da majalisar da kuma irin matsayin da take da shi wajen kiyaye tafarkin juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Hanya guda ta ci gaba da wanzuwa da kuma ci gaban tsarin Musulunci da kuma tabbatar da manufofin juyin juya halin Musuluncin shi ne "samun karfi na hakika a kasar Iran" da kuma "jihadi mai girma" wato rashin mika kai ga makiya.

Haka nan kuma yayin da yake mika godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki saboda yadda aka samu nasarar gudanar da zaben 'yan majalisar kwararru da kyau sannan kuma jama'a suka fito kwansu da kwarkwatarsu don zaban wakilansu a wannan majalisa mai matukar muhimmanci, Jagoran ya bayyana cewar: Majalisar kwararru wata kyauta ce ta Ubangiji, wata cibiya ce mai tasirin gaske, koda ma an rufe ido kan ayyukanta da aka yi bayaninsu cikin kundin tsarin mulki na kasa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana tattaro irin wadannan malamai, masana bangarori daban-daban na ilimin addini da sauransu wadanda kuma mutane suka yarda da su, shi kansa wani lamari ne mai muhimmancin gaske, daga nan sai ya ce: Wannan gungun mutane ma'abota daukaka suna da wani fage mai girman gaske na musayaen ra'ayi da kuma gudanar da ayyuka tare wadanda za su iya yin tasiri mai girma.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kyakkyawar alakar da ke tsakanin malamai membobin wannan majalisa ta kwararru da kuma irin karfin da suke da shi na yin tasiri cikin tunanin al'umma, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Bai kamata 'yan wannan majalisar su zamanto ba sa wani yunkuri sai kawai lokacin gudanar da ayyukansu da suka zo cikin kundin tsarin mulki ba.

Jagoran ya bayyana "musayen ra'ayi da tattaunawa kan batutuwa daban-daban", "ba da himma kan batutuwan da aka sa a gaba", "sanar da matsayar da kuma abubuwan da ya kamata a yi" da kuma "samar da wani fage na tattaunawa da isar da bukatun mutane" a matsayin wasu daga cikin fagagen da majalisar kwararrun take da su na fadada ayyukanta. Daga nan sai ya ce: Matukar aka samu damar tabbatar da wadannan manufofin, ko shakka babu bangarori daban-daban na gwamnati da kuma jami'an gudanarwa za su yi kokari wajen tabbatar da wadannan bukatun.

Har ila yau kuma yayin da yake bayyana cewar wajibi ne tafarki da kuma manufofin majalisar kwararrun su zamanto daidai da tafarki da kuma manufofin juyin juya halin Musulunci, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana: "iko na Musulunci", "'yanci", "'yancin kai", "tabbatar da adalci na zamantakewa", "jin dadin al'umma", "tumbuke tushen talauci da jahilci", "tsayin daka wajen fada da munanan dabi'u, rashawa da cin hanci da lalacewa ta zamantakewa da siyasa da kasashen yammaci suke son shigowa da su" da kuma "tsayin daka wajen tinkarar mulkin mallakan ma'abota girman kan duniya" a matsayin mafiya muhimmancin manufofin juyin juya halin Musuluncin al'ummar Iran.

Jagoran ya bayyana son mulkin mallaka a matsayin wata dabi'a ta ma'abota girman kan duniya daga nan sai ya ce: Yanayin ma'abota girman kai shi ne neman tabbatar da iko da kuma mulkinsu a kan sauran al'ummomi. Duk wata kasa ko kuma al'ummar da ba ta yi fada da hakan ba, to kuwa za ta ci gaba da zama karkashin ikon na su.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar ko shakka babu addinin Musulunci yana fada da zalunci da kuma girman kai don haka sai ya ci gaba da cewa: Koda yake Musuluncin da zai iya irin wannan tsayin daka a gaban ma'abota girman kan na duniya, fada da su da kuma kawo karshensu, shi ne Musuluncin da ya sami damar tabbatar da wani tsari na hukuma wacce take da karfi na soji, siyasa, tattalin arziki, al'adu da kuma kafafen watsa labarai.

Jagoran ya bayyana kiyaye juyin juya hali da cewa ya fi samar da shi wahala, haka nan kuma yayin da yake karin haske kan yadda ya kamata a yi fada da ma'abota girma kai da zalunci na duniya, sai ya ce: makiya al'ummar Iran dai sun fara ne da amfani da karfin tuwa wajen fada da al'ummar Iran da suka hada da tilasta musu kallafaffen yaki na shekaru 8, bore da tashin hankalin da suka faru a farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda, kai hare-hare kan rijiyoyi da cibiyoyin man fetur na Iran da kuma kakkabo jirgin fasinjar Iran, wanda cikin taimakon Ubangiji da kuma hikimar marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma tsayin daka da hakurin al'umma, aka samu nasara a kan makiyan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yakin kwakwalwa a matsayin mataki na gaba na yaki ba kyakkyaftawa da masu tinkaho da karfi na duniyan suka kaddamar kan Iran inda ya ce: ci gaba da sanya takunkumin tattalin arziki, hare-hare na siyasa, bakar farfaganda ta bata sunan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a idon duniya, wasu ne daga cikin mataki na biyu na hare-haren da makiya suka kaddamar a kan Iran, wanda shi din ma bisa taimakon Allah da kuma tsayin dakan al'umma da jami'an gwamnati sun gagara cimma manufar da suke son cimmawa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kokarin yin tasiri a cikin gida a matsayin mataki na uku na irin wadannan hare-haren da suke kai wa wanda yana da hatsarin gaske. Jagoran ya ci gaba da cewa: Ma'abota girman kan dai suna son cimma wadannan manufofi ne ta hanyar kokarinsu na kutsawa da yin tasiri, wadanda su ne: "neman yin tasiri a kan cibiyoyi masu daukar matsaya a Iran", "sauya irin imanin da mutane suke da shi" da kuma "sauya mahanga da lissafin jami'an gwamnati".

Jagoran ya bayyana yada bakar farfaganda da nufin shafa kashin kaji ga tushe da kuma cibiyoyin juyin juya hali irin su dakarun kare juyin juya hali, majalisar kare kundin tsarin mulki, matasa masu riko da addini da malamai masu riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci a matsayin wasu daga cikin hanyoyin da makiya suke amfani da su don cimma manufofinsu, inda ya ce: babbar manufar makiya a wannan yaki na kwakwalwa ita ce share fagen cin kafar gwamnatin Musulunci da raunana irin karfi na cikin gida da ta ke da shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Matukar suka cimma wadannan manufofin sannan kuma suka raba Jamhuriyar Musulunci da tushen karfinta ba, to kuwa kawar da ita ko kuma sauya mahanga da tafarkin da take tafiya a kai ba wani abu ne mai wahala ba. A saboda haka ne nake jaddada cewar rashin biyayya ga makiya da kuma tsayin daka wajen tinkarar bakaken manufofinsu, wani "babban jihadi" ne.

Bayan bayanin tafarkin riko da juyin juya hali na majalisar kwararru, daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: samar da wasu sabbin hanyoyi da gudanar da lamurran addini ta hannun wasu mutane malamai masu karfi da kwarewar fitar da hukunce hukunce na addini da kuma magance cutar da makiya suka haifar da suka hada da "rarrabuwa da rikici na mazhaba da kabilanci", "sabani na kungiyanci" da kuma "haifar da rarrabuwan kai na boge a cikin kasa" wasu ne daga cikin ayyukan majalisar kwararrun.

Don haka sai ya kirayi 'yan majalisar kwararrun da cewa: tsayuwa waje guda (rashin ci gaba) dai ba abu ne mai kyau ba; don haka ku ba wa batun sauyi da ci gaba da nufin kai wa ga manufofin Musulunci da juyin juya halin Musulunci muhimmancin gaske.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ware bangaren karshe na jawabin nasa ne wajen bayanin nauyi da kuma ayyukan da suke wuyan dukkanin jami'an gwamnati a wannan lokaci da ake ciki.

Jagoran ya bayyana tabbatar da karfi na hakika a kasar Iran a matsayin hanya guda kawai ta "tabbatar da wanzuwa, ci gaba da kuma kai wa manufofin juyin juya hali da kuma al'ummar Iran" yana mai cewa: A saboda dukkanin jami'an gwamnati suna da wani nauyi a wuyansu a wannan tafarkin, wanda wajibi ne su sauke shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa karfafa kasar Iran wani lamari ne da zai sanya kwato hakkin da ake da shi hatta daga wajen manyan kasashen duniya masu takama da karfi yana mai cewa: Idan kuwa ba haka ba, hatta raunana da kuma kaskantattun gwamnatoci, za su zamanto suna dagun kai da neman cin kashi wa Iran.

Yayin da yake kawo misalin karbar wani hakki a wajen makiya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: jami'an gwamnatinmu suna fadin cewa a yayin tattaunawar nukliya sun kwato wani hakkinmu sannan kuma bangaren da muke tattaunawar da shi ya amince da hakkin da muke da shi na mallakar fasahar nukiliya; to tabbas an cimma haka ne bayan da Iran ta kai ga karfi, wato samun karfin tace sinadarin uranium zuwa kashi 20 cikin dari. Don kuwa kowa ya san cewa, a bangaren tace uranium, isa ga fasahar tace kashi 20 cikin dari shi ne mataki mafi wahala da sarkakiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana "samar da bututun tace uranium har guda dubu 19", "fara amfani da bututu dubu 10", "samar da bututun tace uranium din zuriya ta biyu da uku da hudu" da kuma "samar da kamfanin samar da sinadarin tace uranium" din a matsayin wasu misalai na irin karfin da Iran ta samu a fagen nukiliya. Daga nan sai ya ce: Makiyin da a baya koda bututun tace sinadarin uranium guda bai yarda Iran ta mallaka ba, to amma bayan da ya fuskanci wannan karfi da tsayin daka na nukiiya daga wajen al'ummar Iran, sai ga shi an tilasta masa amincewa da wannan. A hakikanin gaskiya ba wai Amurka ne ta amince mana da hakan ba, face dai hakkinmu ne muka kwato a wajenta.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kara da cewa: Da yardar Allah a lokacin da aka tabbatar da sakamakon tattalin arziki na dogaro da kai a aikace da kuma tabbatar da karfin tattalin arzikin Iran, to kuwa makiya za su fahimci rashin tasiri da kuma amfanin takunkumin da suke sanya mana.

Ayatullah Khamenei ya bayyana ci gaba da neman an tabbatar da irin wannan karfin a matsayin wani aiki na 'yan majalisar kwararrun.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana tsoron Allah, jaruntaka, basira, fitowa fili a lokacin bukata sannan da kuma rashin damuwa da zargin mai zargi bugu da kari kan kyakkyawar fahimtar makiya da hanyoyin da suke bi wajen cimma manufofinsu a matsayin manyan almaun da suke nuni da riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci.

Jagoran ya bayyana cewar: A wasu lokuta makiya, don cimma manufofinsu, suna aikata wasu ayyuka wadanda a zahiri masu kyau ne, sannan kuma mutane a cikin gida sukan yi maraba da hakan, to amma idan har muka fahimci hakikaninsu, to lalle ba za mu fada tarkon yaufararsu ba.

Kira ta karshe da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wa 'yan majalisar kwararru ita ce yarda da kai da kuma karfin da ake da shi.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musuluncin, sai da shugaban majalisar kwararru Ayatullah Ahmad Jannati ya gabatar da jawabinsa inda yayin da yake mika godiya da kuma jinjina wa Jagoran dangane da sako mai karfafa ruhi da ya aika musu yayin bude majalisar, ya bayyana cewa akwai fahimtar juna da ruhin aiki tare a tsakanin 'yan majalisar.

Har ila yau kuma mataimakin shugaban majalisar na biyu Ayatullah Hashemi Shahrudi shi ma ya gabatar da jawabinsa inda ya gabatar da rahoto kan aikin majalisar da kuma abubuwan da aka gudanar yayin bude ta.

3501306

captcha