IQNA

Malamin Azahar:

Raya Lamarin Ahlul Bait (AS) Shi Ne Kadai Zai tseratar Da Al’umma

23:44 - May 27, 2016
Lambar Labari: 3480453
Bangaren kasa da kasa, Sheikh nadi Albadri daya daga cikin malaman Azhar kuma masoyin Ahlul bait (AS) ya bayyana cewa, yin riko da koyarwar Ahlul bait (AS) ne kawai mafita ga al’ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hubbaren Hussaini cewa, Sheikh Badri Nadi babban malami da ya karba gayyatar da aka aike masa zuwa taron Taratil Sajjadih da ahubbaren ya shirya, ya bayyana aniyarsa ta zuwa taron a hubbaren Imam Hussain (AS) domin gabatar da kasidarsa, tare da bayyana matsayin iyalan gidan manzo da koyi da a matsayin hanyar tsira.

Sayyid Jamaluddin Shahristani babban daraktan kula da ayyukan hulda da jama’a na wannan hubbare mai tsarki ya bayyana sheikh Badruddin Nadi a matsayin babban masoyin Ahlul bait (AS) a kowa ne lokaci.

Ya ce wannan malami yana daga cikin malamai da suke a sahun gaba wajen kokarin ganin an raya taruka da suke da alaka da Ahlul bait (AS) a kasar masar.

Shahristani ya kara da cewa, a zaman da aka gudanar a kasar masar, Sheikh Badruddini ya bayyana cewa, ya zama wajibi kan al’ummar musulmi su raya sha’anin Ahll bait (AS) a kowane lokaci, domin yin hakan yan atattare da samun tsira, da kuma yada koyarwar ma’aiki mai tsira da aminci.

Abin tuni a nan dais hi ne, wannan taro na taratil Sajadiyya za a gudanar da shi ne acikin watanni masu tare da halartar malamai daga sassa na duniya.

3501411

captcha