
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arbynews.com cewa, Sheikh Mnasur Bin Abdulrahman Alshugaibi shugaban cibiyar hardar kur’ani ta kasar ya bayyana cewa wannan mata duk da shekarunta 97 ta samu damar hardace kur’ani a cikin irin wannan yanayi.
Ya ce ta kasance tun tashinta ba ta yi karatu ba, saboda haka ba ta iya karatu da rubutu ba, kuma ta fara hardar a lokacin da shekarunta suka haura 90 a duniya.
Sheikh Mnasur Bin Abdulrahman Alshugaibi ya kara da cewa, cibiyarsu da ke kula da ayyukan karatu da hardar kur’ani a garin Khamis Mashit ta bayar da kyautar ban girma ga wannan mata, wadda ta zama a bin buga misali wajen himma da kuma kwazon da ba shi misiltuwa.