IQNA

Mutane 59 Sun Jikkata A wajen Bude Masallaci Guinea

21:58 - May 29, 2016
Lambar Labari: 3480460
Bangaren kasa da kasa, akalla mutane 59 ne suka jikkata a wajen bude wani masallaci a garin Timbo bayan da suka yi bata kasha da yan sanda.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa Standard Digital cewa, wannan lamari ya faru ne a lokacin da wasu manyan jami’ai suka zo wurin da ake taron bide masallacin, inda jami’an tsaro suka hana mutane shiga, lamarin da ya harzuka sauran mahalarta wurin.

Jama’a sun fara nuna fushinsu da hakan ne ta hanyar yin jifa da duwatsu, amma jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa su, inda mutane suka jikkata.

A cewar Mamadou Kuyati shugaban asibitin garin Timbo, yanzu haka akwai mutane 59 da suke kwance a asibitinsa suna karbar magani sakamakon raunukan da suka samu.

Kimanin kasha 85 cikin dari na mutanen kasar dai musulmi ne, kuma garin Timbo na daga cikin biranan musulmi na wannan kasa ta Afirka.

3501980

captcha