
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin shugaban kasa cewa, Hojjatol Islam Rauhani a lokacin da yake ganawa da malamai daga lardin Azarbaijan ya bayyana cewa, Imam Khomenei (RA) ya tantace hanyar yanci da zama masu cin gishin kai, kamar yadda kuma jagora Ayatollah Khamnei yake ci gaba da tafiya kan wannan tafarki.
Hakan nan kuma ya yaba wa al’ummar azarbaijan, tare da bayyana su a matsayin mutanen da ska bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaki domin kare jamhuriyar muslunci, tare da yin tsayin daka kan Wilayatol Faqih.
A daya bangaren bayaninsa, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, abin mamaki ne yadda masu ikirarin hidima ga Haraimai biyu sun dage wajen biyan bukatun yahudawan sahyuniya ta hanyar hana Iran zuwa hajjin bana domin safke farali.
3502575