IQNA

Kungiyar Jama’at Islami A Masar Ta Halasta Buga Kur’ani Mai Launi

23:36 - May 30, 2016
Lambar Labari: 3480462
Bangaren kasa da kasa, babban mufti na kungiyar Jama’at Islami ya bayar da fatawa da ta sabawa Azhar da kke halasta buga kur’ani mai launi.

Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na Iqna ya hbarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Al’umma Al-akhbariyyah cewa, Abdulakhir Imad babban mai bayar da fatawa na kungiyar jama’at Islami a Masar ya bayyana cewa, babu wani dalili na shari’a da ya hana buga kur’ani mai launi.

A shafinsa na sada zukunta na facebook ya fitar da fatawar cewa, ya halasta a buga ko karanta kur’ani mai launi.

Abdulakhir Imad y ace mafi yawan malamain da sun rika rubuta kur’ni ne tare da yin alamomi masu launi, kuma sun halasta kawata kur’ani da zinari ko azurfa.

Abin tuni a nan shi ne wasu daga cikin kasashen larabawa sun hana buga kr’ani mai launi a kasashensu, kamar su Syria, Lebanon, Masar da kuma UAE.

Kafin wannan lokacin dai Ahmad Abdulaziz Alhaddad babban mai bayar da fatawa na UAE ya amince kan halascin buga kur’ani da rubutu mai launi, amma cibiyar Azhar ta hana hakan a mahangarta.

Cibiyar ta Azhar dai ta nuna damuwa matuka dangane da wannan sabuwar fatawa da shugaban kngiyar Jama’at Islami ya bayar da halasta buga kur’ani mai launi, tare da yin watsi da mahanr cibiyar ta Azhar da ke matsayin bababr cibiyar muslunci a kasar ta Masar.

Kungiyar Jama’at Islami dai ita ce bababr kungiyar salafiyanci da ke dake da akidun wahabiyanci a kasar Masar.

3502117

captcha