
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na baltimor san cewa, an gudanar da wannan shiri ne a jiya Lahadi, domin tunawa da cika shekaru arbain da kafa babbar cibiyar musulunci a wannan gari.
Naim Big shi ne shugaban wannan cibiya ta muslunci, ya kuma bayyana cewa shekaru biyu kenan a jere suna gudanar da wannan shiri, suna bayar da kyautuka matune marassa galihu, domin su ma su bayar da gudunmawarsu wajen ci gaban garin.
Ketty Crowd wata mat ace yar shekaru 68 da haihuwa yar asalin garin ta bayyana cewa, wannan abin da muuslmi suke yi ya kara fito da kyakkyawar fuskar muslunci.
Ta ce an jima ana gaya musu maganganu kan musulmi marassa kan gado, tare da bakanta musulmi a wurinsu, amma wannana bun ya tabbatar musu da cewa muusulmi mutanene na gari, wadanda suk eyin aikin taimako da zuciya guda, ta ce idan sauran mutane za su fahimci haka da an zauna da juna lafiya.
Abin tuni a nan dais hi ne, wannan kwandunan da da musulmi suke rabawa dai sun kunshi kayan marmari da ruwa, abin goge baki, man goge baki, sabulun wanka da wanki.