
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yanarb gizo na Mirsul yaum cewa, wannan gasa an fara ta ne da mutane fiye da 1500, kafin kaiwa ga wannan mataki domin fitar da wadanda za s kara daga karshe.
Muhammad Mahanna daya daga cikin jami’an da suke kula da gasar a masallacin Azahar ya bayyana cewa, wannan gas aba wai ta kebanta da mutanen kasar Masar ba ne kawai, akwai daruruwan yan kasashen ketare da suka shiga.
Yace a koda yaushe cibiyar ta Azhar tana hankoron ganin ta samar da malami ne a dukkanin bangarori na addini.
Kuma an shiya wannan gasa ne tare da hadin gwiwa tsakanin cibiyar ta Azhar da kuma radiyon kasar Masar, inda za a fitar da mtane 10 wadsanda suka fi kyawun sauti da kuma iya karatu.
A matakin farko makaranta fiye da dubu daya ne suka shiga gasar daga sassa na lardunan kasar, sai kuma mutane 500 yan kasashen ketare.
Daga cikin malamai masu alkalanci a wannan gasa akwai malaman Azahar da kuma na radio kur’an, sai kuma wasu manyan makaranta wato sheikh Ahamad Ahmad Nu’ainu’a, Shiekh Abdulfattah Taruti, da kuma Mahmud Alkhesht.