IQNA

Za A Gina Kwalejin Ilmomin Kur’ani A Kasar Sudan

23:56 - May 31, 2016
Lambar Labari: 3480466
Bangaren kasa da kasa, za a gina wani kwaleji na koyar da ilmomin kur’ani mai tsarki a yankin Al-nasr da ke birnin Khartum na kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na KUNA cewa, wannan cibiya za a gina ta ne tare da daukar nauyincibiyar Al-rahma ta kasar Kuwait.

Amal Al-bili ministan kula da harkokin al’adu na kasar sudan ya bayyana cewa, wanann kwaleji zai kunshi bangarori daban-daban na koyar da ilmomin kur’ani mai tsarki da ya hada da harda da tajwidi da sauransu.

Fahad Alkendri makarancin kur’ani dan kasar Kuwait ya bayyana cewa, yana farin ciki matuka da dora tubulin fara wanann aiki na gina kwalejin kur’ania kasar Sudan.

Inda ya bayyana cewa, yana da sha’awar yadda al’ummar kasar Sudan suke mayar da hankali matuka wajen harkokin da suka shafi kur’ani da ilmominsa, wanda kuma ko shakka babu wannan kwaleji zai taimaka matuka wajen samar da hanyoyi na zamani domin koyon ilmomin kur’ani.

Taron dora tubulin ginin wanann kwaleji dai ya samu halartar wasu daga cikin ministocin gwamnatin Sudan, da kuma wasu daga cikin jami’ai na cibiyar da za ta aiwatar da wanann aiki.

Abdullah Ma’atuk shi ne mai bayar da shawara kan harkokin addini ga sarkin Kuwait, wanda shi ma ya halarci wurin.

3502633

captcha