IQNA

Taro Mai Taken “Mutumin Da Ya Kawo Canji A Gabas Ta Tsakiya” A Italiya

23:34 - June 01, 2016
Lambar Labari: 3480467
Taro Mai Taken “Mutumin Da Ya Kawo Canji A Gabas Ta Tsakiya” A Italiya
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken “Mutumin Da Ya Kawo Canji A Gabas Ta Tsakiya” Imam Khomenei (RA) a birnin Rome na kasar Italiya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin cibiyar yada al’adun muslunci cewa, ana shirin gdanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan tuna da shekaru 27 da rasuwar marigayi Imam Khomenei (RA) a 15 Khordad wanda wata cibiya za ta dauki nauyin shiryawa a birnin Rome na kasar Italiya mai taken "Mutumin Da Ya Kawo Canji A Gabas Ta Tsakiya” a katafaren otel na Best Western Blu Hotel.

Ali Reza Jalali shi ne shugaban cibiyar binciken harkokin muslunci a birnin na Rome, wanda kuma shi ne ya shirya gudanar da wannan zaman taro, ya bayyana cewa akwai manyan masana nha kasar Italiya da za su halarci wurin kuma za su gabatar da makalolinsu, daga ciki har da Clodio Moti, Adolfo Morganti, Paylio Rada da kuma Josephe Alillo, da Abul Fazl Imami shugaban cibiyar Imam Mahdi (AJ) sai kuma jakadan Iran a Rome Akbar Kuli.

Daga cikin makalolin da za a gabatar akwai wadanda za su Magana kan rayuwarsa, da kuma bangaren siyasa, da tasirinsa wajen wayar da kan wasu daga cikin a’ummomin turai kan muslunci, sakonnin Imam Khomenei (RA) zuwa ga Gobache da Pop, rubuce-rubucen Imam Khomenei (RA) da kuma gudunmawarsa wajen gina sabon tarihin kasar Iran.

3503323

captcha