
Sheikh Mahdi Alsumaidai babban malamin Ahlu sunna mai bayar da fatawa a Iraki, ya bayyana hana maniyyatan kasar Iran zuwa aikin hajjin bana saboda siyasa a matsayin wani babban lamari na kunya ga duniyar musulmi.
Ya ce batun aikin hajji lamari ne na al'ummar musulmi baki daya, ba na wani mutum ba ne ko wata masarauta ko wani gida, saboda haka babu wata hujja ko wani dalili da zai sanya a hana wata kasa zuwa safke farali saboda banbancin siyasa tsakaninta da wata masarauta, wannan bas hi da alaka da aikin hajji.
Sheikh Sumaidai ya ce yana ganin da ya kamata sarakunan masarautar iyalan gidan Saud su sake tunani da salo kan wanann lamari, su ajiye batun banbancin mahangar siyasa tsakaninsu da Iran kan batun hajji kamar yadda ake a da, hakan shi ne maslaha ba ne ga musulmi baki daya.