IQNA

Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Kasa A Mauritania

23:06 - June 03, 2016
Lambar Labari: 3480475
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar harda da karatun kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a Mauritania akaro na biyar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albadil cewa, tun jiya ne aka gudanar da taron bude wannan gasa a birnin Nuwakshot fadar mulkin kasar.

Sayyid Abdullah Wuld Yakub wuld Hurmatullah shi ne babban darakta na hukmar radio da talabijin na kasar tare da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati gami da manyan malamai duk sun halarci wurin taron.

Ya ce yanzu makaranta da mahardata 3397 ne daga koina cikin kasar suka taru domin karawa da juna a wannan gasa ta kur’ani mai tsarki.

Sayyid Muhammad Almukhtar Wuld Mbala shugaban kwamitin malami mai bayar da fatawa a kasar, ya gabatar da jawabinsa awajen bude taron wannan gasaa a jiya, inda ya ce ko shakka babu, bada muhimmanci ga harkokin kur’ani yana da matkar muhimmanci ga musulmi, musamman ma a wannan lokaci da ake amfani da shi domin wanke kwakwalen mutane a samu tsatsauran ra’ayi da ke kai su ga ta’addanci.

3503626

captcha