
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, cibiyar Al-safa da ke gudanar da ayyukan alkhairi ita ce za ta dauki nauyi shiya gudanar da wanann gasa a Qatif.
Gasar dai ta hada da yan mata da kuma yara maza matasa, inda matasa maza za su gudanar da tasu gasar daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Ramadan, sai kuma yan mata daga ranar 11 zuwa 13 ga watan azumin Ramadan mai alfarma.
Daga cikin abubuwan da wannan gasa za ta kunsa har da karatu da kuma hardar kur'ani, gami da tafsiri, sai kuma rubutun kur'ani, wanda ya hada da salo daban-daban na fasaha, kuma za agudanar da gasar ne a masallacin Siddiqat Zahra (SA) da ke garin Safawi na lardin Qatif.