
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na beliefnet cewa, musulmi da wadanda ba musulmi za su iya shiga wanann kamfe, inda za su iya tura ayoyin da suke bukata zuwa ga shafin domin samun Karin bayani.
Wadanda suke da sha’awa abin da za su yi shi ne, su shiga ta wannan hanya #ttQuran, inda za su samu wurin da za su saka ayar da suke bukata.
Daga cikin abubuwan da shafin key i shi ne karanta ayar da aka aiko da kuma yin tarjama a cikin harshen trance, haka nan kuma idan mutum yana bukatar Karin bayani kan wasu abbuwa da suka danganci wanann ayar zai bayyanawa.
Hakan nan kuma awrin za su iya tatatuanawa da juna kan wannan ayar da abubuwan da ta kunsa da kuma dalilin da yasa mutum ya zabi wanann aya daga kur’ani mai tsarki.
Babbar manufar wannan kamfe dai ita ce yada koyarwar kur’ani mai tsarkia tsakanin musulmi na Amurka, da kuma wadanda ba muuslmi ba da suke son sanin wani dangane da wannan littafi mai girma.