IQNA

An Gina Masallaci A Babbar Hedikwatar ‘Yan Sanda A Ghana

23:51 - June 06, 2016
Lambar Labari: 3480482
Bangaren kasa da kasa, an gida wani bababn masallacia a hedikwatar yan sandan kasar Ghana a birnin Akra fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, an gina wannan masallaci nea cikin babbar hedikwatar yan sandan na kasar Ghana wadda ke da mazauni a fadar mulkin kasar da ke birnin Akra

Babban sufeton yan sanda a kasar Ghana zantarwasa da jaridar Daiky Graphic ya bayyana cewa, babbar manufar gina wannan masallaci dai ita ce bayar da dama ga ‘yan sanda musulmi su gudanar da aikinsu cikin sauki.

Wannan masallaci dai ya kunshi wurin salla gami da wuraren gudanar da taruka da karatu inda aka gina babban dakin karatu wanda aka saka littafan addinin muslunci a cikinsa.

Sufeton yan sandan ya ce wannan m,asallaci ba wai wurin gudanar da salla ne kawai ba, har ma taruka da suka shafi yan sanda muuslmi dangane da abubuwan da suke yi da kuma abin da ya shafi musulmi da bukatrsu ga tsaro nay an sanda.

Kasar Ghana dai tana daga cikin kasashen da mazauinasu akasari mabiyta addinin kirista ne, amma kuma musulmi su ne na biyu ta fuskar yawa.

Bisa la’akari da tasirin da msulmi suke da shia kasar, wannan ya sanya ake basu mhimmanci matuka a cikin dukkanin harkokin da suka shafikasa da al’ummarta.

Kuma hakan yan ada babban tasiri a kasar da mafi yawan mazaunanta kiristoci kumaka gina babban masallaci a cikin babbar hedikwatar yan sanda ta kasar.

Tuna cikin shekara ta 1916 ce dai aka ggina babbar hedikwatar yan sanda a birnin Akra, ama babu wani wuri da aka kebance ma musulmi domin gudanar da ibada.

Wani dan kasar Lebanon ne dai ya dauki nauyin gina wannan masallaci domin samun lada daga ubangiji.

3504099

captcha