IQNA

An Halasta Ma Masu Kai Hari A Yemen Shan Azumi

23:56 - June 07, 2016
Lambar Labari: 3480486
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa a masarautar iyalan gidan Saud ya halasta wa masu kaddamar da hari kan al'ummar kasar Yemen shan azumi.
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habara cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na 
Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, babban mai baiwa sarakunan masarautar iyalan gidan Saud fatawa Abdulaziz Al-sheikh ya fitar da wata sabuwar fatawa, wadda a ciki yake cewa sojojin kasarsa da kuma wadanda suke mara musu baya, za su shan azumi, domin kuwa suna a matsayin masu yaki fisabllahi ne, ya halsta su ajiye azumi a fagen daga.

Haka nan kuma ya fitar da wata fatawar wadda ya ce yan kasar wadanda suke kartua  waje dole ne suka cika azumi koda kuwa tsawon rana ya kai sa'oi 22 a kasar da suke, babu wani uzuri a kansu na ajiye azumi, matukar dai za su iya tantance da rana.

Wannan fatawa dai ta jawo cece ku ce daga sassa daban-daban na kasashen larabawa, inda suke ganin hakan a matsayin wani lamari na shishigi a cikin dokokin ubangiji.

captcha