
Bangaren kasa da kasa, Ibrahim Ja’afari ministan harkokin wajen kasar Iraki ya bayyana cewa yan ta’addan daesh sun tayar bama bamai a masallatai tare da kone kur’anai.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Alwasat cewa, ministan harkokin wajen kasar Iraki ya bayyana cewa yan ta’addan daesh ISIS sun tayar bama bamai a masallatai tare da kone kur’anai da dama.
Ya ce yan ta’addan suna kai hare-hare kan mai uwa da wabi da hakan ya hada da mata da kanan yara da mata, babu banbanci a wurinsu a tsakanin sunna da kuma shia domin kowa a wurinsu kafiri ne matukar dai baya a cikinsu.
Ibrahim Ja’afari ya kara da cewa yan ta’addan mabarnata da basu da wata alaka da muslunci balanta koyarwar ko kuma koyarwa manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa.
Hak nan kumaya yi kira ga masu daukar nauyin yan ta’adda daga cikin kasashen larabawa musaman ma masu akidar kafirta musulmi, da su sake yin nazari kana bin da suke yi na cutar da musulmi.
Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar ta Iraki ya yi kira da akawo yan ta’addan da suke iko da Falluja ba tare da wani bata lokaci ba.