
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoli cewa, wasu gungun masu fasahar ayyukan zanen hannu da rubutu ne mata suke gudanar da wannan aikin a cikin masallatai.
Wanann aiki dai ya zo nea cikin wannan lokaci da ake gudanar da azumin watan ramadana mai alfarma, inda suke gyara masallatai na birnin tare da kawata su da ayyuka na fasahar zane da kuma rubutun ayoyin kur'ani mai tsarki.
Goldane Argin Jan wadda take jagorantar wannan aiki ta bayayna cewa, hakika aikin nasu yana da matukar muhimamnci, domin kuwa aiki ne na karfafa zukata wajen kawata wuraren ibadar ubangiji.
Kuma jama'a sun gamsu suna murna da hakan, saboda haka za su ci gaba da yi domin ganin wuraren ibadar ubangiji sun kawatu suna karbar baki masu bauta, domin samun lada daga Allah madaukakin sarki.
3505430