Bangaren kasa da kasa, wata tashar talabijin ta kasar Mauritania ta dakatar da watsa fim na annabi Yusuf (AS) sakamakon sukar da take sha a yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta
cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabi 21 cewa, tashar
talabijin ta Shanqit ta dakatar da watsa fim na annabi Yusuf (AS) sakamakon
sukar da take sha a shafukan yanar gizo daga wasu yan kasar kan hakan.
Wannan tasha tana watsa shirin ne tun daga
lokacin da aka fara azumin watan Ramadan mai alfarma, ammakuma daga bisani kuma
wasu sun shiga sukar wannan shirin na annabi Yusuf (AS) da take watsawa.
Daga cikin wadanda suka shiga sukar wannan
shiri da wannan tasha take gudanarwa na saka fim din annabi Yusuf (AS) akwai
mutanen gari masu wata mahanta ta dabam da aka dora su a kanta, kamar yadda
kuma malamansu na akida su ma sun shiga lamarin suna haramta musu kallon fim
din.
Tare da yin kira ga wannan tasha da ta
dakatar da wannan shiri, lamarin da yasa ala tilas wannan tasha ta bi abin da
wadannan mutane suke bukata saboda tsoron kada ayi mata illa.