IQNA

Nuna Goyon Bayan Al’ummar Bahrain Ga Sheikh Ali Salman

23:41 - June 10, 2016
Lambar Labari: 3480501
Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Bahrain na nuna goyon bayanta ga babban sakataren jam’iyyar wifaq sheikh Ali Salman tare da yin kira da a sake shi.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, mutanen kasar Bahrain sun fito kan tituna suna jerin gwano na nuna goyon bayanta ga babban sakataren jam’iyyar wifaq sheikh Ali Salman wanda ake tsare da shi bisa zaluncin mahukuntan kasar, tare da yin kira da a gaggauta sakinsa.

Masu jerin gwanon sun bayyana tsare malamin da ake yi a matsayin wani naui na zalunci da danne hakkokin bil adama da masarautar mulkin mulukiyya ta kasar take yi ba ji ba gani.

Tun a ranar 28 ga watan Disamban shekara ta 2014 ce dai mahukuntan kasar ta Bahrain suka kame sheikh Ali Salman da sunan cewa za su yi bincike aknasa, amma daga bisani sai suka sanar da yanke masa hukuncin dauri.

Sun daure shi shekaru hudu a gidan kaso a cikin shekara ta 2015, amma kuma daga bisa a ranar 30 ga watan Mayn da ya gabata, kotun masautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain ta sanar da cewa, ta kara tsawon shekarun daure sheikh Salman daga shekaru 4 zuwa 9 a gidan kaso.

Kama sheikh Ali Salman dai ya fskanci kakakusar ska daga kasashn duniya, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya da suka ahada da kungiyar afuwa da sauransu.

3505610

captcha